Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Xi Jinping ya zanta da firaministan kasar Rasha
2019-06-06 20:46:46        cri

A yau Alhamis 6 ga watan nan ne, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya zanta da firaministan kasar Rasha Dmitry Medvedev a birnin Moscow. Yayin zantawar ta su, shugaba Xi ya bayyana cewa, a halin da ake ciki yanzu haka, alakar Sin da Rasha ta shiga wani sabon matsayi, kuma cikakkiyar dangantakar kawance kasashen biyu daga dukkanin fannoni na kara bude sabon shafin ci gaba a tarihi.

Shugaban na Sin ya ce, yayin da ake fuskantar yanayi mai sarkakiya a fannin alakar kasashen duniya, musamman ma matakai na rashin adalci da ake dauka kan kasashe masu tasowa domin dakile ci gaban su, yana da matukar muhimmanci ga Sin da Rasha su karfafa bunkasa cikakkiyar dangantakar kawancensu daga dukkanin fannoni, da hadin gwiwar su, domin kare moriyar su da ta al'ummun su, tare da kare zaman lafiyar duniya, da daidaito da ci gaba.

A nasa bangare, Mr. Medvedev, ya ce sanarwar da shugabannin kasashen biyu suka sanyawa hannu a jiya na da matukar muhimmanci, duba da yadda ta fayyace nasarar da aka samu ta bunkasa kawancen kasashen biyu zuwa wani sabon matsayi a tarihi. Ya ce a halin yanzu, daidaikun kasashe, ba tare da lura da sakamako ba, suna karya ka'idojin kasa da kasa, da na cudanyar sassa daban daban, suna kuma kakabawa wasu kasashe takunkumi, tare da nuna karfin tuwo, matakin da ya kawo nakasu ga ci gaban tattalin arzikin duniya, ya kuma gurgunta hada hadar cinikayyar duniya. Ya ce irin wadannan matakai na su, ba sa kunshe da hangen nesa kuma suna cutarwa.

Mr. Medvedev ya kara da cewa, ya dace Rasha da Sin su ci gaba da bunkasa hadin gwiwar su daga dukkanin fannoni, su yi aiki tare domin magance kalubalen dake gaban Rasha, da Sin, da ma sauran sassan kasa da kasa, kana su himmatu wajen tabbatar da zaman lafiya da ci gaban duniya baki daya.(Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China