Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kasar Sin da MDD za su gina cibiyar binciken manyan bayanai a Hangzhou
2019-06-04 11:28:45        cri
Gwamnatin kasar Sin da MDD, sun sanar jiya a Shanghai cewa, za su hada hannu wajen gina cibiyar binciken manyan bayanai a birnin Hangzhou dake gabashin kasar Sin.

Shugaban hukumar kididdiga ta kasar Sin Ning Jizhe da mataimakin Sakatare Janar na MDD a bangaren harkokin tattalin arziki da al'umma, Liu Zhenmin, sun rattaba hannu kan yarjejeniyar fahimtar juna kan ginin cibiyar binciken manyan bayanai ta farko da MDD za ta gina tare da hadin gwiwar wata kasa.

Birnin Hangzhou ne ke kan gaba a kasar Sin wajen bincike da amfani da manyan bayanai, inda yake da kamfanoni da dama a wannan fannin.

Liu Zhenmin ya ce manyan bayanai na da matukar muhimmanci wajen cimma ajandar ci gaba mai dorewa na MDD da ake son cimmawa zuwa 2030, musammam wajen taimakawa kasashe masu tasowa da ba su da karfin binciken manyan bayanai, domin a damada su a fannin sarrafa bayanai na duniya.

Cibiyar ta Hangzhou za ta gudanar da kwasa-kwasai domin horar da kasashe masu tasowa hanyoyin amfani da manyan bayanai. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China