2019-06-06 12:17:56 cri |
A yankin Ningxia Hui mai cin gashin kansa dake shiyyar arewa maso yammacin kasar Sin, akwai mabiya addinin musulunci sama da miliyan 2.5. Ma Weilin wani dattijo ne mai shekaru 76 a duniya, ya bi sahun jama'ar yankin inda tun da sanyin safiya ya tafi masallacin Idi da misalin karfe 8 a.m. na safe a masallacin Yinchuan, babban birnin yankin.
"Yanayin bikin yana da matukar kayatarwa kasancewar rayuwar mutane tana kara kyautatuwa," in ji shi.
Bikin Idin karamar sallah ya kasance wani biki ne da aka amince da shi a yankin Xinjiang Uygur mai cin gashin kai, inda mutane ke yin hutun wuni guda don halarta bikin. Ana janye kudin haraji ga masu tuka motoci mallakinsu a daidai lokacin hutun bikin sallar Idin.
Sawutjan Abulim, shi ne limanin masallacin Liudaowan dake Urumqi, ya ce an yiwa masallacin kwaskwarima tare da sanya kayayyki kamar ruwan fanfo, ruwa zafi, na'urar sanyaya daki da intanet, wanda gwamnati ke daukar nauyi, Musulmi suna samun damar gudanar da ibadunsu cikin kwanciyar hankali, in ji limanin. (Ahmad Fagam)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China