Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Amurka ta lalata tsarin ciniki maras shinge na duniya bisa ga takaddamar ciniki da ya tayar
2019-06-05 11:28:46        cri
Bisa la'akari da yadda Amurka ke ta kara ruruta takaddamar ciniki a tsakaninta da kasar Sin tare da daukar matakai kan kamfanonin kasar ta Sin, baki da suka halarci taron tattauna hadin gwiwar sassan kasa da teku bisa shawarar "ziri daya da hanya daya" da ya gudana daga ranar 2 zuwa 4 ga wata a birnin Chongqing na kasar Sin sun bayyana cewa, matakan da Amurka ta dauka sun lalata tsarin ciniki maras shinge na duniya, wadanda ka iya haifar da dimbin hasara ga duniya baki daya, kuma ita Amurka ma ba za ta amfana ba, don haka, ya kamata a daidaita sabanin da ake fuskanta ta hanyar yin shawarwari.

Tsohon firaministan kasar Faransa Dominique de Villepin da ya halarci taron ya ce, kasancewar Amurka da Sin manyan kasashe biyu mafiya karfin tattalin arziki a duniya, kasashen duniya da dama na dogara da su ta fannin tattalin arziki, don haka, takaddamar ciniki da Amurka ta tayar za ta iya haifar da mummunan tasiri ga tattalin arzikin duniya. Ban da kara kakaba wa kasar Sin haraji, Amurka ta kuma ba da umurnin kayyade harkokin ciniki da suka shafi kamfanin Huawei na kasar Sin, kamfanin da ya kasance daya daga cikin manyan kamfanonin sadarwa a duniya, musamman ta fannin fasahar 5G, kuma tsaron kasa hujja ce kawai ga Amurka kan matakan da ta dauka.

Har wa yau, mataimakin firaministan kasar Cambodia, Hor Nam Hong ya bayyana cewa, takaddamar ciniki da kasar Amurka ta tayar ba lalata moriyar kasashen duniya da suka hada da Sin da Cambodia kadai za ta yi ba, har ma da haifar da hasara ga kamfanonin Amurka da ma manoman kasar, lamarin da ya shaida cewa, babu wanda zai amfana daga takaddamar ciniki da ma manufar kariyar ciniki. (Lubabatu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China