Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
#Takaddamar cinikin Sin da Amurka# Amurka ce ke da alhakin kawo cikas ga tattaunawar ciniki tsakaninta da Sin
2019-06-02 12:01:23        cri

Zarge zargen da gwamnatin Amurka ke yi kan kasar Sin na kawo cikas bashi da tushe balle makama, a cewar takardar bayani mai taken matsayin da Sin ta dauka kan tattaunawar ciniki da tattalin arzikin Sin da Amurka, wadda ofishin yada labarai na majalisar gudanarwar Sin ta fitar a yau Lahadi.

Kasar Sin ta bayyana cikakkiyar adawa da matsayin da Amurka ta dauka na kashin kanta na kara kudaden harajin kwastam, kuma Sin ta bayyana matsayinta cewa tilas ne ta mayar da martani.

Sin ta nanata cewa, wajibi ne a kafa yarjejeniyar cinikayya bisa adalci da moriyar juna. Kasar Sin ba za ta amince da duk wasu matakai da za su lahanta babbar moriyarta ba, in ji takardar bayanin.

"Daya daga cikin sharrudan mu'amalar cinikin shi ne, wajibi ne Amurka ta janye dukkan karin harajin kwastam da ta sanyawa kayayyakin da kasar Sin ke shigarwa kasarta, kana tilas ne Amurkar ta yi la'akari da kayayyakin da Sin ke saya daga wajenta domin tabbatar da ganin an samu daidaito a bisa yarjejeniyar da aka tsara domin biyan muradu da moriyar bangarorin biyu," in ji takardar.(Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China