Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
#Takaddamar cinikin Sin da Amurka# Sin ba za ta amince da matakin lalata moriyarta ba
2019-06-02 12:04:09        cri

Takardar bayanan gwamnatin kasar Sin da aka fitar yau ta jaddada cewa, ba zai yiyu ba kasar Sin ta amince da matakin lalata moriyar kasarta ba, kana tana fatan za a daidaita matsalar ta hanyar yin tattaunawa, a maimakon kara buga harajin kwastam.

Kasar Sin ta nanata cewa, idan ba za a iya daidaita dukkanin matsalolin ta hanyar daddale jarjejeniya guda daya ba, to dole ne sassan biyu su amince da abubuwan da aka rubuta a cikin yarjejeniyar, ta yadda za a tabbatar da moriyar sassan biyu.

Takardar ta bayyana cewa, kasar Sin ta nuna rashin amincewa ga matakin da Amurka ta dauka na kara buga haraji kan kayayyakin kasar Sin da ake shigar da su kasar Amurka, har ta mayar da martani domin kiyaye moriyar kanta, yanzu haka domin kara kiyaye moriyar al'ummun kasashen biyu wato Sin da Amurka, kasar Sin za ta kara yin hangen nesa, amma ba za ta ji tsoron matsin lambar da ake yi mata ba ko kadan, a shirye take ta yi shawarwari, haka kuma a shirye take ta yi yakin cinikayyar.(Jamila)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China