Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
#Takaddamar cinikin Sin da Amurka# Ba a daidaita sabani tsakanin Sin da Amurka saboda matsin lambar Amurka ba
2019-06-02 11:48:54        cri

Takardar bayanin da gwamnatin kasar Sin ta fitar a yau Lahadi mai taken "matsayin da kasar Sin ta dauka kan tattaunawar tattalin arziki da cinikayya dake tsakaninta da Amurka" ta bayyana cewa, duk da cewa, sassan biyu wato Sin da Amurka sun riga sun cimma matsaya kan yawancin batutuwan dake shafar yarjejeniyar tattalin arziki da cinikayya tsakaninsu, amma saboda Amurka tana son samun karin moriya, sai ta dauki matakin matsin lamba da nuna fin karfi wato ba ta so ta soke harajin da ta kara bugawa kan kayayyakin da ake shigar da su kasar ta Amurka tun bayan da sassan biyu suka fara fama da takaddamar tattalin arziki da cinikayya, har ta nace ga rubuta abubuwan dake shafar harkokin cikin gidan kasar Sin a cikin yarjejeniyar, duk wadannan batutuwa sun hana sassan biyu daddale yarjejeniyar.

Takardar ta kara da cewa, kasar Sin ta mayar da martani ta hanyar kara buga haraji kan kayayyakin Amurka da ake shigo da su kasar ta Sin domin kiyaye hakki da moriyarta.(Jamila)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China