Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin ta fitar da takardar gwamnati kan matsayin da ta dauka yayin tattaunawar ciniki tsakaninta da Amurka
2019-06-02 11:13:25        cri

Yau Lahadi ofishin watsa labarai na majalisar gudanarwar kasar Sin ya fitar da takardar gwamnati game da matsayin da ta dauka yayin da take gudanar da tattaunawar cinikayya da kasar Amurka, makasudin matakin shi ne domin gabatar da cikakken bayani kan gudanar da tattaunawar cinikayya tsakaninta da Amurka, tare kuma da bayyana matsayin da take dauka kan batun.

Wannan karo na biyu ne da kasar Sin ta fitar da takardar bayanan gwamnati kan batun game da tattaunawar cinikayya dake tsakaninta da Amurka tun bayan da ta fitar da takardar bayanai irin wannan ta farko mai taken "Hakikanan abubuwa game da takaddamar tattalin arziki da cinikayya dake tsakanin Sin da Amurka da matsayar da kasar Sin ta dauka" a watan Satumban bara.

A cikin takardar bayanan gwamnatin, an yi nuni da cewa, tun bayan da sabuwar gwamnatin Amurka ta fara rike mulki a kasar a shekarar 2017, sai ta fara daukar matakai a jere domin haifar da illa ga sauran kasashen duniya wadanda ke gudanar da harkokin cinikayya da ita, misali kara buga haraji ga kayayyakin da ake shigo da su kasar ta Amurka. Daga watan Maris na shekarar 2018, gwamnatin Amurka ta tayar da takaddamar cinikayya da kasar Sin, har kasar Sin ta ga tilas ta mayar da martani domin kiyaye babbar moriyar kasa da al'ummunta, a sa'i daya kuma, har kullum kasar Sin ta nace kan matsayinta na daidaita matsala ta hanyar yin shawarwari, a don haka ta yi tattaunawa kan tattalin arziki da cinikayya da Amurka har sau da dama, ta yadda sassan biyu za su gudanar da huldar tattalin arziki da cinikayya dake tsakaninsu cikin lumana.

Kana takardar, gwamnatin kasar Sin ta nuna cewa, kwanakin baya Amurka ta sanar da cewa, za ta kara buga haraji ga kayayyakin Sin da ake shigo da su kasar, ko shakka babu lamarin zai lalata huldar tattalin arziki da cinikayya, kasar Sin ba za ta amince da matakin ba, shi ya sa ta mayar da martani a kan lokaci domin kiyaye hakki da moriyarta ta halal.

Takardar ta jaddada cewa, game da takaddamar tattalin arziki da cinikayya dake tsakaninn kasashen biyu, kasar Sin tana fatan za su daidaita takaddamar ta hanyar yin hadin gwiwa, tare kuma da daddale wata jarjejeniya mai moriyar juna, amma dole ne a gudanar da hadin gwiwa bisa tushen adalci, ba zai yiyu kasar Sin ta amince da matakin da zai lalata moriyar halal ta al'uumunta ba.(Jamila)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China