Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
#Takaddamar cinikin Sin da Amurka#Matakin Amurka na kara haraji ba zai amfanar da ita kanta ba
2019-06-02 11:14:33        cri

Gwamantin kasar Amurka ta sanya karin harajin kwastam ga kayayyakin da kasar Sin ke shigarwa zuwa Amurka, matakin dake haifar da koma baya tare da yin illa ga hadin gwiwar ciniki da zuba jari tsakanin bangarorin biyu, kana da kawo illa ga bunkasuwar tattalin arzikin kasashen biyu har ma da duniya baki daya, kamar yadda wata takardar bayani mai taken matsayar kasar Sin game da tattaunawar cinikayya da tattalin arziki tsakanin Sin da Amurka wadda ofishin majalisar gudanarwar kasar Sin ya fitar a yau Lahadi.

Matakin kara harajin na Amurka ya yi sanadiyyar raguwar adadin kayayyakin da kasar Sin ke shigawar zuwa kasar Amurkar, inda ya ragu da kashi 9.7 bisa 100, bisa na makamancin lokacin bara a cikin watanni hudun farko na shekarar 2019, inda ya ragu cikin watanni biyar a jere, kamar yadda takardar bayanan ta bayyana, inda aka samu bayanan dake shafin intanet na babbar hukumar kwastam ta kasar Sin.

Bugu da kari, sakamakon martanin da kasar Sin ta yi inda ta kara kudaden harajin kayayyakin da Amurkar ke shigarwa zuwa kasar Sin, kayayyakin da Amurka ke shigarwa kasar Sin sun yi matukar raguwa a cikin watanni takwas a jere.

Bisa la'akari da yadda ake ci gaba da fuskantar takaddamar ciniki tsakanin Sin da Amurka, kungiyar WTO ta rage adadin hasashen da ta yi na karuwar tattalin arzikin duniya na shekarar 2019 daga kashi 3.7 bisa 100 zuwa kashi 2.6 bisa 100, in ji takardar bayanan, kamar yadda kungiyar WTO ta wallafa a shafinta na intanet game da rahoton hasashen da ta yi.(Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China