![]() |
|
2019-05-30 14:32:21 cri |
Shugaban bankin jama'ar kasar Sin, wato babban bankin kasar Yi Gang, ya bayyana yau a nan Beijing cewa, tun daga shekarar bara, hukumomin hada-hadar kudi masu ruwa da tsaki, sun aiwatar da matakan bude kofar Sin ga kasashen waje, wadanda shugaba Xi Jinping na kasar Sin ya sanar a yayin taron shekara-shekara na dandalin tattaunawar Asiya ta Boao a watan Afrilun bara.
Babban bankin Sin ya gabatar da wasu sharuddan ba da iznin shiga kasuwannin kasar, tare da kawar da bambanci a tsakanin hukumomin hada-hadar kudi na gida da waje, don haka hukumomin hada-hadar kudi masu jarin waje sun samu ci gaba sosai wajen shiga kasuwannin Sin. Masu jarin waje suna ta shiga kasuwar kasar ta Sin. (Tasallah Yuan)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China