Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Tu Jiayao ya koma garinsa da samar da gudummawa a fannin bada ilmi
2019-05-28 11:25:35        cri
Yankin Kaizhou dake birnin Chongqing, yana daya daga cikin yankuna masu talauci a birnin, wanda aka fi samun tsaunuka da tuddai a yankin, da kawar da talauci a shekarar 2018. A wannan yanki, akwai wani kamfanin kimiyya da fasaha na Shuteng, wanda ya yi nazari, da samar da hidimar na'urorin zamani dake makarantu. Wannan ne kamfanin da Tu Jiayao mai shekaru 42 da haihuwa ya koma garinsa ya kafa a watan Oktoba na shekarar 2017.

Tu Jiayao ya bayyana cewa, yanzu lokaci ne na yin kirkire-kirkire a fannin kimiyya da fasaha, amma wasu na'urorin makarantu na yankuna masu talauci ba su da bambanci da na lokacin da na yi karatu a da. Don haka, yana son komawa gida ya samar da gudummawa a fannin bada ilmi a yankin Kaizhou.

A shekarar 2018, an shigar da na'urorin bada ilmi da kamfaninsa ya samar zuwa makarantun yankin, wadanda malamai da yara suka yi farin ciki da samun su. (Zainab)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China