Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kasar Sin ta taya Mutharika murnar sake zama shugaban Malawi
2019-05-30 10:11:36        cri

A jiya Laraba ne kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Lu Kang, ya ce kasar Sin ta taya Arthur Peter Mutharika murnar sake zama shugaban kasar Malawi. Ya ce, Sin ta yi imani da cewa, Malawi za ta kara samun ci gaba karkashin shugabancin mista Mutharika.

Ranar 27 ga wata, kwamitin zaben Malawi ya sanar da sakamakon zaben da ya gudana a kasar, inda shugaba mai ci, kuma shugaban jam'iyyar DPP Arthur Peter Mutharika ya sake lashe zaben shugabancin kasar, sakamakon samun kuri'un da yawansu ya kai kaso 38.57. Yanzu haka dai shugaban zai fara wa'adin aikinsa na biyu na shekaru 5.

Lu Kang ya bayyana a nan Beijing cewa, kasar Sin na sa muhimmanci kan raya hulda a tsakaninta da Malawi. Tana kuma son hada kai da Malawi wajen aiwatar da sakamakon da aka samu, yayin taron koli na Beijing na dandalin tattauna hadin gwiwa tsakanin kasashen Sin da Afirka, da muhimmin daidaito da shugabannin 2 suka cimma, a kokarin inganta mu'amala da hadin gwiwa tsakanin kasashen 2 a sassa daban daban, don kara kawo wa kasashen 2 da jama'arsu duka alherai. (Tasallah Yuan)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China