Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kungiyar likitocin Sin ta baiwa wani asibitin Rwanda kyauta
2019-05-30 11:04:53        cri
Kungiyar likitocin Sin ta 19 da ke tallafawa aikin jinya a kasar Rwanda, ta mikawa asibitin Masaka dake birnin Kigali fadar mulkin kasar wasu magunguna, da na'urorin aikin likitanci da gwamnatin kasar Sin ta bayar a matsayin gudunmowa.

Karamin jakadan kasar Sin mai kula da ayyukan tattalin arziki da kasuwanci dake kasar Rwanda Wang Jiaxin, ya halarci bikin mika kayayyakin a jiya Laraba, inda ya gayawa manema labaru cewa, duk wata kungiyar likitocin kasar Sin da ta zo kasar Rwanda, ta kan mika wasu kayayyaki ga asibitocin wurin, don taimaka musu warware matsaloli irinsu karancin magunguna, da na'urorin da ake bukata wajen aiwatar da aikin jinya.

Jami'in ya ce, an dade ana hadin gwiwa tsakanin kasashen Sin da Rwanda a fannin aikin kiwon lafiyar jama'a, kana ana ganin habakar hadin gwiwar sassan biyu a shekarun nan.

A nasa bangare, shugaban asibitin Masaka Marcel Uwizeye, ya ce za a yi amfani da magungunan, da sauran kayayyakin da kasar Sin ta bayar wajen kula da majiyyata, da horar da ma'aikata, ta yadda za a samu damar daidaita yanayin da jama'ar kasar ke ciki a fannin kiwon lafiya. A madadin asibitinsa, shugaban ya mika godiya ga kasar Sin, kan yadda take hadin kai da kasar Rwanda a fannin aikin jinya, da jinjinawa likitocin kasar Sin bisa kokarin aikinsu. (Bello Wang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China