Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Masu gabatar da shirin CGTN da Fox sun tattauna batun takaddamar ciniki
2019-05-30 11:03:38        cri

 

 

A safiyar yau Alhamis, bisa agogon Beijing, mai gabatar da shiri a gidan telabijin na kasar Sin CGTN Malama Liu Xin, da takwararta ta gidan telabijin din Fox na kasar Amurka, Malama Trish Regan, sun yi musayar ra'ayi a wani shiri na kafar kasuwanci ta Fox fuska da fuska, dangane da batun takaddamar ciniki da ake samu tsakanin Sin da Amurka.

A cikin shirin, Trish Regan ta tambayi Liu Xin, dangane da ra'ayinta game da shawarwarin da ake yi tsakanin Sin da Amurka, don daidaita takaddama da ciniki, inda Malama Liu ta amsa cewa, ba ta da majiya a cikin hukumomin kasashen 2, don haka ba ta san ainihin matsayin da aka cimma wajen gudanar da shawarwarin ba. Duk da haka tana ganin cewa gwamnatin kasar Sin ta riga ta bayyana matsayinta sarai.

Game da batun ikon mallakar fasahohi, Madam Liu ta ce, idan za a iya amfanar juna, da koyon fasahohin juna, to, babu matsala a ba da damar sayen ikon mallakar fasahohi. Ta haka kowa zai samu moriya. Liu ta yi amfani da wani misali wajen bayyana ra'ayinta, ta ce dalilin da ya sa ta iya Turancin Ingilishi shi ne, domin tana da wata malama ba'amurkiya wadda ta koyar da ita yaren.

Sa'an nan dangane da yadda wasu mutane ke son ganin kasar Sin ta yi watsi da matsayinta na wata kasa mai tasowa, Liu Xin ta ce, kasar Sin ba ta son zama kan tsohon matsayinta na wata kasa maras karfi, kuma tana son samun ci gaba, amma wani abu mai muhimmanci shi ne, yadda ake fahimtar kalmar "wata kasa mai tasowa". (Bello Wang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China