Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An bukaci gwamnatin Najeriya da ta ci gajiyar yarjejeniyar cinikayya da kudaden juna da ta cimma da kasar Sin
2019-05-22 09:24:27        cri

Shugaban kungiyar 'yan canji ta Najeriya Aminu Gwadabe, ya yi kira ga gwamnatin kasarsa da ta ci gajiyar yarjejeniyar cinikayya da kudaden kasashen juna da suka cimma da kasar Sin don kara karfin kudin kasar Najeriya wato Naira.

Shugaban ya yi wannan kiran a birnin Legas, cibiyar kasuwancin kasar. Ya kuma shawarci babban bankin kasar, da ya zurfafa kunshin yarjejeniyar da kasar Sin da ma fadada matakan fitar da kayayyaki zuwa kasar Amurka ta yadda za a kara fadada hanyoyin samun kudaden musayar ketare na kasar.

Ya ce, ya kamata Najeriya ta mayar da hankali wajen fadada hanyoyinta na samun kudaden musayar ketare ta hanyar bunkasa yadda 'yan kasar dake ketare ke aiko kudade gida, don bunkasa tattalin arzikin kasar da kara karfin asusun ajiyar kudaden ketare na kasar.

A watan Afrilun shekarar 2018 ne, babban bankin al'ummar kasar Sin, ya kulla yarjejeniyar da Najeriya. Ana sa ran za a yi mu'amalar da ta kai Yuan biliyan 15, kwatankwacin dalar Amurka biliyan 2.17 da kudin kasar Najeriya wato Naira biliyan 720 cikin shekaru uku.

Za kuma a iya kara tsawon wa'adin yarjejeniyar ta hanyar fahimtar juna, matakin da ya sanya Najeriyar zama kasa ta uku a nahiyar Afirka, bayan Afirka ta kudu da Masar, da ta sanya hannu kan wannan yarjejeniya da kasar Sin.

Haka kuma Najeriyar ce kasa ta farko a nahiyar Afirka, da take amfani da kudin kasar Sin RMB a cikin asusun ajiyar kudadenta na ketare.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China