Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kasuwar hannun jarin New York ta ragu sosai
2019-05-14 15:02:47        cri

Sakamakon takaddamar cinikayya dake tsakanin Sin da Amurka, mizanin DJIA wato Dow Jones Industrial Average gami da mizanin Nasdaq a kasuwar hannayen jari ta New York a Amurka sun ragu kwarai da gaske a ranar 13 ga wata. Bangarori daban-daban a Amurka, ciki har da bankin Goldman Sachs da kamfanonin bada shawara ga harkokin cinikayya sun bayyana cewa kara harajin kwastam zai yi babbar illa ga tattalin arzikin Amurka.

A ranar 13 ga wata, yayin da aka bude kasuwar hannun jarin New York, mizanin DJIA ya ragu da kashi 1.7 bisa dari, shi kuma mizanin Nasdaq ya ragu da kashi 2.4 bisa dari. Zuwa lokacin da aka rufe kasuwar a ranar, mizanin DJIA ya ragu da kashi 2.9 bisa dari, sa'annan kuma mizanin Nasdaq ya ragu da kashi 3.4 bisa dari idan aka kwatanta da na ranar 12 ga wata.

A halin yanzu, kafofin watsa labaran tattalin arzikin Amurka na maida hankali sosai kan batun tankiyar cinikayyar dake tsakanin Sin da Amurka. Akwai kuma masanan Amurka da dama wadanda suka bayyana damuwarsu kan tsanantar halin da ake ciki, a cewarsu, abun da gwamnatin Amurka ta yi, wato kara sanya haraji kan kayayyakin da kasar Sin ke shigarwa kasar ba zato ba tsammani, zai tsananta takaddamar cinikayya tare kuma da haifar da tarnaki ga farfadowar tattalin arzikin Amurka. Har wa yau kuma, wasu bankunan zuba jari da kamfanin bada shawara ga harkokin cinikayya sun bullo da rahoton bincike kan tasirin da kara sanya kudin haraji zai yi ga tattalin arzikin Amurka.

Bisa rahoton da bankin Goldman Sachs ya fitar a kwanakin baya, an ce, kamfanoni gami da masu sayayya a Amurka, suna shan wahalar abun da gwamnatinsu ta yi na kara kudin haraji kan kayayyakin Sin, inda a cewarsu, bai kamata a dorawa kasar Sin laifi ba. Rahoton ya kuma ce, idan tankiyar cinikayyar ta ci gaba da tsananta, yawan GDP na Amurka zai ragu da kashi 0.4 bisa dari.

Wani kamfanin bada shawara ga harkokin cinikayya na Amurka mai suna The Trade Partnership mai hedkwata a Washington, shi ma ya fitar da irin wannan rahoton bincike, inda ya nuna cewa, kara sanyawa kayayyakin kasar Sin haraji da gwamnatin Amurka ta yi daga kashi 10 zuwa 25 bisa dari, zai rage guraban ayyukan yi da yawansu ya kai miliyan daya zuwa watan Nuwambar bana, kuma matsakaicin yawan kudin da iyalan Amurka za su kashe a duk shekara zai karu da dala 767. Rahoton ya kuma ce, idan gwamnatin Amurka ta kara sanya haraji kan sauran kayayyakin kasar Sin da darajarsu ta kai dala biliyan 300, zai rage adadin yawan guraban ayyukan yi miliyan biyu a Amurka, har ma yawan GDPn Amurka a bana zai ragu da kashi 1.01 bisa dari.

Duba da yakin cinikayyar da Amurka ta kaddamar kan kasar Sin da ma sauran wasu kasashe, kasashe da dama sun kara sanya haraji kan kayayyakin da Amurka take fitarwa a matsayin wani matakin ramuwar gayya. Bisa alkaluman da ma'aikatar ayyukan gona ta Amurka ta fitar a kwanakin baya, an nuna cewa, akwai amfanin gona da dabbobin gida masu tarin yawa wadanda ba'a iya sayar da su ba a kasar.

Rika sanyawa kayayyakin kasar Sin haraji da gwamnatin Amurka ta yi, ba illa ga ayyukan kamfanoni gami da zaman rayuwar al'ummar kasar kadai zai yi ba, har ma da yin mummunan tasiri kan tattalin arzikin kasar. Haka kuma a watanni bakwai da suka gabata, yawan gibin cinikin gwamnatin Amurka ya zarce dala biliyan 530, wanda ya karu da kashi 38 bisa dari idan aka kwatanta da na shekarar bara. An kuma yi hasashen cewa, a shekara ta 2019, yawan gibin cinikin Amurka zai kai dala tiriliyan 1.1.

Ita kasar Sin ta maida martani kan yakin cinikayyar da Amukra ta kaddamar, inda ta sanar da cewa, tun daga ranar 1 ga watan Yunin bana, za ta sake kara wa wasu hajojin Amurka da darajarsu ta kai dala biliyan 60 da tuni aka riga aka kara haraji kansu harajin kaso 25 da kaso 20 da kuma kaso 10 bisa dari. Kwamitin kula da ka'idojin sanya haraji na majalisar gudanarwar kasar Sin, ya bayyana cewa, daukar mataki na kara sanyawa hajojin Amurka haraji, wani martani ne da kasar Sin ta mayar don yaki da abun da Amurka ta yi na nuna bangaranci da ra'ayin bada kariya ga harkokin kasuwanci. Kasar Sin tana kuma fatan cewa, Amurka za ta sake dawowa turba madaidaiciya wato gudanar da shawarwari da kasar Sin kan harkokin tattalin arziki da cinikayya, da yin kokari tare da Sin don cimma wata yarjejeniya bisa tushen girmama juna. (Murtala Zhang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China