in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ya kamata Sin da Amurka su dauki babban nauyin dake wuyansu
2019-04-04 15:27:16 cri

A yayin da yake ganawa da tawagar majalisar dattawa dake kunshe da wasu tsofaffin shugabannin kasashe a kwanakin baya a birnin Beijing, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya jaddada cewa, dangantakar kasa da kasa na da alaka sosai da zaman lafiya da kwanciyar hankalin duniya, shi ya sa kamata yayi manyan kasashen su dauki babban nauyin dake rataye a wuyansu, musamman dangantakar Sin da Amurka, wadda ta zama daya daga cikin dangantakar kasa da kasa mafiya muhimmanci a duk fadin duniya.

A yayin ganawar, shugaba Xi ya ce yana fatan kasarsa da Amurka zasu yi kokarin daidaita sabanin ra'ayi da fadada hadin-gwiwa tsakaninsu, tare kuma da raya huldarsu bisa tushen samun daidaito da hadin-gwiwa. Haka kuma a ranar 15 ga watan Fabrairun bana, shugaba Xi Jinping ya gana da wakilin cinikayyar Amurka Robert Lighthizer gami da ministan kudin kasar Steven Mnuchin wadanda suka jagoranci tawaga don halartar shawarwarin Sin da Amurka kan harkokin tattalin arziki da cinikayya a zagaye na shida a Beijing, inda ya ce, kasashen biyu na da babbar moriya ta bai daya a fannonin shimfida zaman lafiya da neman wadata a duniya, kana kuma bunkasa dangantakarsu yadda ya kamata ta dace da moriyar jama'arsu. Har wa yau, a ranar 1 ga watan Disambar bara, a ganawar shugabannin Sin da Amurka, Xi ya jaddada cewa, Sin da Amurka na da muhimmin nauyi iri daya a fannonin tabbatar da zaman lafiya da neman bunkasuwa a duniya, kana hadin-gwiwa zabi ne mafi kyau gare su.

Kalmar "nauyi" wata muhimmiyar kalma ce da shugaba Xi ya sha ambatawa a sau da dama yayin da yake zancen dangantakar Sin da Amurka. Sin da Amurka manyan kasashe biyu ne masu karfin tattalin arziki a duniya, wadanda suke taka muhimmiyar rawa wajen habaka tattalin arziki da kiyaye zaman doka da oda gami da tinkarar kalubale a duniya. Don haka makomar dangantakar Sin da Amurka na shafar duk duniya baki daya.

A halin yanzu, duniya na fuskantar damammaki da dama da kirkire-kirkiren kimiyya da fasaha gami da sauye-sauyen masana'antu ke kawowa, har ma tana fuskantar wasu kalubale da dama, ciki har da ra'ayin bada kariya ga harkokin cinikayya, da rashin karfin ci gaban tattalin arziki da sauransu. A don haka ya kamata manyan kasashen biyu wato Sin da Amurka su dauki nauyin jagorantar sauran kasashe wajen shawo kan kalubaloli da neman damammaki, a maimakon neman bunkasar kansu kadai.

Duba da mabambantan tsari da al'adu da halin ci gaban kasa, ana samun wasu sabanin ra'ayi tsakanin kasashen Sin da Amurka. Amma daukar wasu matakan da ba su dace ba, ba zasu taimaka wajen warware sabanin ba, har ma zasu kawo tarnaki ga bunkasuwar tattalin arzikin duniya, kamar kara harajin kwastam da bada kariyar harkokin kasuwanci. Wani masanin tattalin arzikin Amurka mai suna Howard Shatz ya yi gargadin cewa, idan kasar Sin ko kasar Amurka ta gamu da tawayar tattalin arziki, duk duniya ma zata ji radadin. Shi yasa ya kamata kasashen biyu su lalibo bakin zaren daidaita sabaninsu ta hanyar da ta dace, ta yadda tattalin arzikinsu zai bunkasa sannu a hankali.

Shugaba Xi ya kuma jaddada cewa, hadin-gwiwa shine zabi mafi kyau ga Sin da Amurka, kuma bunkasa huldarsu lami-lafiya ya dace da moriyar jama'arsu baki daya.

Har kullum kasar Sin tana nuna himma da kwazo wajen fadada hadin-gwiwa da sauran kasashen duniya. Sin ta gabatar da shawarar "ziri daya da hanya daya" don kafa wani sabon dandalin hadin-gwiwar kasa da kasa, da tura sojojinta sama da dubu talatin don shiga cikin ayyukan shimfida zaman lafiya na MDD a duk duniya, tare kuma da aiwatar da manufar yin gyare-gyare a gida da bude kofa ga kasashen waje, al'amuran da suka shaida cewa, kasar Sin na sauke babban nauyin dake wuyanta a fannonin da suka shafi tabbatar da zaman lafiya da bada gudummawa da kiyaye zaman doka da oda a duniya. A ziyararsa kasashen Turai, shugaba Xi ya kuma yi kira ga kasashe daban-daban da su yi aiki tukuru wajen gudanar da harkokin duniya. Wannan wani sabon kokari ne da kasar Sin ke yi wajen raya kyakkyawar makomar bil'adama ta bai daya, kana sabon bayani ne ga babban nauyin da Sin ke da shi.

A matsayinta na kasar dake tasowa mafi girma a duniya, akwai mutane miliyan 16.6 wadanda har yanzu ke fama da kangin fatara a kasar Sin, amma Sin bata taba kaucewa sauke nauyin dake wuyanta ba, har ma tana namijin kokarinta wajen yin aiki. Amurka, a matsayinta na kasa mai karfin tattalin arziki mafi girma a duniya, ya zama dole ta sauke nauyinta a fannoni daban-daban. A halin yanzu, ana gudanar da shawarwarin tattalin arziki da cinikayya tsakanin manyan jami'an Sin da Amurka a zagaye na tara a Washington, kamata yayi bangarorin biyu su daidaita sabani da fadada hadin-gwiwa tare kuma da farfado da imanin duk duniya tare.(Murtala Zhang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China