Wunderman ya kuma jaddada bukatar cewa, ya kamata alaka tsakanin kasashen biyu ta kasance ta hadin gwiwa. Ya kuma amince cewa, idan aka yi maganar fannin fasahar kere-kere, tilas za a samu takara tsakanin Sin da Amurka, kuma haka lamarin ya gada cewa, sabbin matsaloli ko wasu takaddama za su kunno kai.
Jami'in ya kara da cewa, hanya mafi dacewa ta magance wannan batu, ita ce tattaunawa da musayar ra'ayoyi, da tuntubar juna ba tare da wata rufa-rufa ba. Haka kuma abubuwa da dama sun hada sassan biyu fiye da abubuwan da suka raba su. Hanya mafi kyau da warware wadannan matsaloli. Ita ce narzartar kowace matsala filla-filla.
Ya ce, ya kamata mu daina sanyawa juna haraji, ko kafa shingen cinikayya, ko nuna yatsa. Duk wadannan ba za su haifar da da mai ido ba.(Ibrahim)