Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Masu sa ido na MDD sun halarci janyewar dakarun Houthi daga tashoshin ruwan Hodeidah
2019-05-13 13:07:38        cri
Jami'an sa ido na MDD sun ganewa idanunsu janyewar dakarun Houthi na kasar Yemen, daga tashoshin ruwan nan uku dake birnin Hodeidah. Rahotanni sun ce dakarun na Houthi, sun janye daga tashoshin Salif da Ras-Issa da Hodeidah, a ranar Lahadi.

Shugaban tawagar tsare-tsare ta ficewar dakarun Michael Lollesgaard, ya fitar da wata sanarwa, wadda a cikinta ya ce a ranar farko da aka tsara ficewar dakarun na Houthi komai ya gudana cikin nasara.

Wata sanarwar ta daban da ofishin wakilin musamman na babban magatakardar MDD game da Yemen Martin Griffiths ya fitar, ta ce bayan ficewar dakarun, an mika ikon tashoshin ruwan ga jami'an tsaron bakin teku domin tabbatar da doka da oda.(Saminu Alhassan)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China