lafiya1903.m4a
|
'Yan makarantar firamare, midil, da sakandare, har ma dalibai su kan yi hutu ne bayan karewar zangon karatu. A cikin irin wannan lokacin hutu, su kan ci su kuma sha fiye da kima, musamman ma yayin da ake murnar bukukuwa a lokacin hutu. Saboda haka akwai bukatar iyaye su mai da hankali kan yadda yaransu suke ci da sha a wannan lokaci.
Masu nazari na kasar Amurka sun kaddamar da wani rahoto dake cewa, kananan yara su kan yi kiba nan da nan a lokacin hutun zangon karatu. Watakila babban dalilin da ya sa haka shi ne domin kananan yara su kan dade zauna a kan kujera maimakon motsa jiki, kana su kan ci kayan kwalama fiye da kima a lokacin hutu.
A wani nazari da aka yi kan 'yan makarantar Amurka fiye da dubu 18, masu nazarin sun auna tsayin wadannan yara da nauyin su a ko wane zangon karatu daga shekarar 2010 zuwa shekarar 2013.
Masu nazarin sun gano cewa, mizanin BMI na wadannan yara ya karu a lokacin da suke hutu. Mizanin BMI, mizanin awon nauyin mutum ne a kilogiram a raba da tsayin mutum bisa sikwaya mita. A kan yi amfani da mizanin a duk fadin duniya.
Masu nazarin sun yi karin bayani da cewa, wadannan 'yan makarantar su kan bi ajandar da aka tsara musu a yayin da suke karatu a makarantu. Su kan motsa jiki a kan ka'ida, su kan ci abinci a kai a kai, lamarin da yake taimakawa wajen tabbatar da ganin mizanin na BMI ya yi daidai. Amma a lokacin hutu fa? Ba su bin ajandar da aka tsara. Sa'an nan kuma watakila ba a sa ido kansu yadda ya kamata. Su kan dade zaune a kan kujera, tare da cin kayan kwalama da yawa, lamarin da ya haddasa kananan yara 'yan makaranta masu tarin yawa yin kiba a lokacin hutu bayan karewar zangon karatu.
Masu nazarin sun jaddada cewa, sun gudanar da wannan nazari ne domin yi wa iyaye gargadi, a don haka, ya zama tilas su yi taka tsan-tsan kan karuwar dalilan da suke haddasa kananan yaransu yin kiba a lokacin hutu bayan karewar zangon karatu, alal misali, raguwar lokacin barci, karuwar lokacin kallon telebijin, rashin isasshen motsa jiki, cin abubuwa ta hanyar da ba ta dace ba.
Wasu kwararru sun ba da shawarar cewa, ko a lokacin hutu bayan karewar zangon karatu, ko a lokacin da yara ke karatu, kamata ya yi iyaye su karfafawa 'ya'yansu gwiwar yin barci a kan lokaci, su kuma dauki a kalla awa guda suna motsa jiki a ko wace rana, kana kuma tsawon lokaci da suka shafe suna yin wasa da na'urorin laturoni bai wuce awoyi guda 2 ba, lamarin da zai amfana wajen hana 'ya'yansu yin kiba da kuma taimaka musu yin rayuwa ta hanyar da ta dace. (Tasallah Yuan)