in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Motsa jiki na rabin awa a ko wace rana yana iya tsawaita rayuwar dan Adam
2019-03-11 14:19:56 cri

Yin yawo, da tafiya zuwa wajen aiki, ko kuma yin aiki a gida, da duk wata hanyar da kake so wajen motsa jiki, idan ka dauki a kalla rabin awa kana motsa jiki a ko wace rana, ko kuma a kalla awoyi 2 da rabi a ko wane mako, hakan na iya kare mutane daga kamuwa da ciwon zuciya da kuma barazanar mutuwa.

Wannan shi ne sakamakon nazari da masana kiwon lafiya daga kasashen Canada da Sin suka kaddamar a kwanan baya.

An gudanar da wannan nazari ne a kan mutane dubu 130 daga kasashe 17 na duniya, wadanda shekarunsu suka wuce 35, amma ba su wuce 70 a duniya ba. Sakamakon nazarin ya shaida cewa, a maimakon zuwa gidan motsa jiki, idan mutum na tafiya wajen aiki a kafa,ko yana kewayawa bayan ya ci abincin rana, ko kuma yana yin aikin gida, muddin yana motsa jiki na kimanin rabin awa a ko wace rana, ko kuma awoyi 2 da rabi a ko wane mako, hakan na iya taimakawa wajen rage barazanar kamuwa da ciwon zuciya da kashi 20 cikin dari, kana zai rage barazanar mutuwa da kashi 28 cikin dari. Sa'an nan idan mutane suka yi tafiya da sauri na fiye da minti dari 7 da 50 a ko wane mako, hakan na iya rage barazanar mutuwa da kashi 36 cikin dari.

Masu nazarin sun yi nuni da cewa, babu tantama motsa jiki a gidan motsa jiki yana da kyau sosai. Amma mutane sun fi samun saukin zuwa aiki a kafa, da kewayawa bayan a ci abinci, da yin aiki a gida, wadanda suke iya motsa jiki a ko da yaushe kuma a ko ina suke so.

Har ila yau masu nazarin sun yi nuni da cewa, yanzu haka masu fama da talauci da ke zaune a sassa daban daban na duniya, da wuya sosai su bi hanyoyin yin rigakafin kamuwa da ciwon zuciya, kamar kara cin kayayyakin lambu da 'ya'yan itatuwa ko kuma su sha wasu nau'o'in magunguna. Amma tafiya a kafa ba ya bukatar kashe kudi, wanda kuma yake iya amfanawa lafiyar mutane.

Hukumar kiwon lafiya ta kasa kasa wato WHO ta ba da shawarar cewa, ya kamata baligai wadanda shekarunsu suka wuce 18 amma ba su wuce 64 a duniya ba su ware awoyi 2 da rabi a ko wane mako suna motsa jiki. Duk da haka masu nazarin sun ce, rubu'in al'ummar duniya ba su kai wannan matsayi ba tukuna. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China