in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kyautata shirin fasalin birni da zirga-zirga yana taimakawa wajen inganta lafiyar mazauna wurin
2017-03-13 07:30:38 cri

Shahararriyar jaridar nan ta Lancet da ake wallafawa a kasar Birtaniya ta kaddamar da rahoton wasu nazarce-nazarce a kwanan baya, inda a cewarsu, idan aka kyautata shirin fasalin manyan birane da sufuri, to, hakan zai taimaka wajen rage gurbata muhalli da karfafa gwiwar mazauna wurin ta yadda za su kara sha'awar yin tafiya da kafa da hawa keke, wanda hakan a karshe zai inganta lafiyarsu.

Wani masana daga jami'ar Melbourne ta kasar Australiya da reshen jami'ar California a San Diego ta kasar Amurka su ne suka jagoranci wadannnan nazarce-nazarce da aka gudanar dangane da shirin fasalin birni, sufuri da lafiyar dan Adam. Sun yi karin haske da cewa, yanzu haka a cikin dukkan mutanen da ke rayuwa a duniyarmu baki daya, fiye da rabinsu ne suke zaune a birane, kana kuma za a saurin raya birane nan da shekaru masu zuwa.

Masanan da suka gudanar da nazarce-nazarcen suna ganin cewa, karuwar yawan mutane tana kara haifar da matsin lamba ga harkokin sufuri, yayin da girman birane yake ta karuwa, wannan ya sa tsawon hanyar da mazauna wurin suke bi wajen kaiwa da kamowa a tsakanin gida da wurin aiki yana ta karuwa, lamarin da ya sanya su kara yin amfani da motocinsu, wanda a karshe dai, za a kara fuskantar gurbatar muhalli da kuma hadurran mota da yawa, hakan zai kawo illa ga lafiyar mazauna birni.

Masanan sun yi bayani da cewa, yayin da ake tsara fasalin birni, yana da kyau a karfafa gwiwar mazauna wurin su rika tafiya da kafa, ko hawa keke, ko kuma shiga manyan motocin al'umma, tare da rage yawan yin amfani da motocinsu na kansu. Kamata ya yi a yi kokarin ganin mazauna wurin suna zuwa kantuna da sauran gine-ginen ba da hidima kamar asibiti, gidan waya, da kafa. Haka kuma yana da kyau a kara mayar da hankali wajen raba yankin da mutane suke aiki da kuma yankin da suke rayuwa. Wajibi ne a rage yawan wuraren ajiye motoci da kara kudin ajiye motoci. Ya kamata a kyautata manyan ababen more rayuwa ta fuskar sufuri, a kokarin tabbatar da tsaron lafiyar jama'a yayin da suke tafiya da kafa da kuma tuka mota.

Sakamakon ka'idojin da suka ambata a baya da kuma kara yin amfani da gonaki ta hanyar da ta dace, ya sa masanan suka fito da wani salon fasalin raya birni, inda suka yi amfani da salo raya biranen Melbourne, London, Boston, Copenhagen, Delhi da Sao Paulo, da nufin tabbatar da samun sakamako bayan da aka kyautata fasalin biranen.

Sakamakon tantancewar ya nuna mana cewa, bayan da aka kyautata fasalin wadannan birane 6, lafiyar mazauna wurin ta samu ingantuwa, musamman ma yawan wadanda suka kamu da ciwon zuciya da na magudanar jinni zuwa zuciya ya ragu sosai, sa'an nan mazauna biranen suna kara motsa jiki, yayin da aka rage gurbatar muhalli wadda bangaren sufuri ke haddasawa. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China