in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Aikin dare ya fi kawo illa ga lafiyar mata sama da maza
2017-02-06 09:19:38 cri

Kwanan baya, wata jaridar kwalejin nazarin kimiyya ta kasar Amurka, ta kaddamar da wani sakamakon nazari, wanda ya nuna cewa, aikin dare ya fi kawo illa ga kwarewar kwakwalwar mata wajen fahimta, sama da yadda abun yake ga maza.

Domin gano ko akwai bambanci a tsakanin maza da mata a fannin samun illa a kwarewar kwakwalwarsu wajen fahimta, sakamakon yin aiki da dare, masu nazari daga jami'ar Surrey ta kasar Birtaniya sun gayyaci masu aikin sa kai maza 16, da mata 18, domin su yi kwanaki 10 suna rayuwa a cikin wasu dakuna, wadanda hasken rana daga waje ba ya shiga cikin su, kana babu agogo a ciki, ta yadda masu aikin sa kan ba sa iya sanin lokaci a cikin wadannan kwanaki 10.

A cikin wadannan dakuna, an tsawaita wa'adin da masu aikin sa kan suka dauka na yin barci zuwa farkawa daga barcin, har zuwa awoyi 28, a maimakon guda 24, don haka agogon kwakwalwar masu aikin sa kan sun hargitse, hakan da ya yi kama da yadda sukan yi a aikin dare, ko kuma irin yadda suke fama da bambancin lokaci sakamakon tafiya cikin jirgin sama.

A lokacin da masu aikin sa kan, suka farka daga barci, a kan gudanar da bincike a ko wadanne awoyi 3 kan su, inda akan tambaye su game da yadda suke ji a hankalinsu, kamar ko suna da kuzari, ko suna jin barci. Ana kuma gwada kwarewar kwakwalwarsu wajen fahimta, kamar ko suna iya mai da hankali kan wani abu, ko suna iya motsa jikinsu yadda ya kamata, ko suna iya tunawa da wani abu dangane da aikinsu. Sa'an nan a yayin da suke barci, masu nazarin sun yi amfani da na'ura wajen sa ido kan yanayin kwakwalwar wadannan masu aikin sa kan.

Sakamakon nazarin ya shaida cewa, sauyawar agogon kwakwalwar bil Adama yana kawo illa ga dukkan maza da mata, amma illar da mata suke samu ta fi wadda maza suke samu da tazara mai yawa. An ce mata ba sa iya nuna kwazo wajen fahimta da sanyin safiya, wato lokacin da aka kammala aikin dare.

A cikin wata sanarwar da masu nazarin daga jami'ar Surrey ta kasar Birtaniya suka fitar, sun nuna cewa, wannan ne karo na farko da aka tabbatar da cewa, akwai bambanci a tsakanin maza da mata a fannin illar da suke samu, sakamakon sauyawar agogon kwakwalwar bil Adama. Kuma mai yiwuwa ne aikin dare zai haifar da illa ga kwarewar dan Adam a fannonin tunawa da abubuwa, da tunani da motsin hankali. Kaza lika kuma, watakila mata sun fi samun irin wannan illa sakamakon yin aikin dare, sama da takwarorin su maza. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China