in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kara cin abincin garin alkama zalla yana taimakawa wajen rage yawan mutuwar mutane
2017-01-16 08:13:09 cri

Abincin garin alkama zalla na kunshe da yawan sinadaran bitamin, da kuma sinadaran dake taimakawa wajen narkar da abinci a jikin mutum, lamarin da yake taimakawa wajen kiwon lafiyar jikinmu, da kuma kare mu daga kamuwa da cututtukan zuciya da na magudanar jini da ciwon sankarar hanji.

Kafofin yada labaru na kasar Jamus sun ruwaito rahotannin nazari guda 2 dake cewa, cin abincin garin alkama zalla ya na iya rage yawan mutuwar mutane, musamman ma wadanda ke mutuwa sakamakon cututtukan zuciya da na magudanar jini da ciwon sankara.

Rahoton wata kungiyar nazari ta jami'ar Harvard ta kasar Amurka ya yi bayani da cewa, in an kwatanta wadanda ba sa cin abincin garin alkama zalla ko kadan, yawan mutuwar mutanen da ke cin abincin garin alkama zalla mai giram 48 a ko wace rana ya ragu da kashi 20 cikin dari.

kana yawan mutuwarsu sakamakon kamuwa da cututtukan zuciya da na magudanar jini da ciwon sankara ya ragu da kashi 25 cikin dari, da kuma kashi 14 cikin dari.

Wani rahoto na daban daga wata kungiyar nazari ta kwalejin koyon kimiyya da fasaha ta kasar Birtaniya ya bayyana cewa, in an kwatanta wadanda ba su ci abincin garin alkama zalla, yawan mutuwar mutanen da su kan ci abincin garin alkama zalla mai giram 90 a ko wace rana ya ragu da kashi 17 cikin dari, kana yawan mutuwarsu sakamakon kamuwa da cututtukan zuciya da na magudanar jini da ciwon sankara ya ragu da kashi 22 cikin dari, da kuma kashi 15 cikin dari.

Rahoton ya kara da cewa, abincin garin alkama zalla na iya rage yawan mutuwar mutane sakamakon kamuwa da ciwon sassan jiki masu taimakawa numfashi, da cututtuka masu yaduwa, da kuma ciwon sukari.

Wadannan kungiyoyin nazari 2 sun bada shawarar cewa, abincin garin alkama zalla na iya rage kibar dake taruwa cikin jini da hawan jini, suna kuma iya sanya mutane su ji koshi cikin sauki, ta haka, mutane ba za su rika cin abinci da yawa ba.

Sannan sun ce Kamata ya yi a ilmantar da al'umma muhimmancin amfanin ko cin abincin garin alkama zalla.

Ban da haka kuma, masu nazari daga kungiyar nazarin ciwon sankara ta kasar Denmark suna ganin cewa, kara kashe kudi kan sayen abincin garin alkama zalla zai ba da babban tasiri mai kyau kan kiwon lafiyar al'umma sosai. Yanzu kasar ta Denmark tana tafiyar da wani aiki, a wani kokarin ganin an samu ninkuwar yawan abincin garin alkama zalla da 'yan kasar za su rika ci cikin shekaru 10 masu zuwa. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China