in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Gurbatacciyar iska tana kawo wa mutane babbar barazanar shanyewar jefen jiki
2017-03-05 12:34:44 cri

A kwanakin baya ne, wata kungiyar nazari ta kasa da kasa ta kaddamar da rahoton bincikenta, wanda ke nuna cewa, a shekarar 2013, sulusin raguwar tsawon ran mutane sakamakon shanyewat gefen jiki yana da nasaba da gurbatacciyar iska, muna iya cewa, gurbatacciyar iska wata babbar barazanar ce ga shanyewar gefen jiki dan-Adam.

Wadannan masu nazari daga kasashen New Zealand, Amurka, Sweden da Birtaniya sun kimanta yadda matsalar shanyewar gefen ta adabi kasashe fiye da 100 daga shekarar 1990 zuwa shekarar 2013, daga cikin bayanan da aka tattara dangane da wannan matsala da ake fama da ita a duk duniya,masanan sun yi nazari a kan wasu abubuwa 17 wadanda ake gani sune suke haddasa barazanar kamuwa da matsalar shanyewar gefen jiki, ciki had da yanayin cin abincin mutane, da rashin motsa jiki, da kuma muhallin da suke rayuwa, ko suna fama da gurbatacciyar iska, da dai sauransu.

Masu nazarin sun gano cewa, a cikin batutuwan da suka shafi muhalli, gurbatacciyar iska ta fi haifar da illa. Gurbatacciyar iska da muka ambata a nan ita ce gurbatacciyar iska a waje da kuma cikin daki. A kan yi amfani da ma'aunin tantance inganci iskar shaka wato PM 2.5 wajen auna tsananin gurbatacciyar iskar shaka a wajen daki, yayin da kona abubuwa masu tauri ya kan gurbata iskar da ake shaka a cikin daki. A kasashe masu tasowa, ana kamuwa da shanyewar gefen jiki ne ta hanyar gurbatacciyar iskar da ake shaka.

Ban da gurbatacciyar iska, batutuwan da suka sa mutane su kamu da wannan matsala ta shanyewar gefen jiki sun hada da hawan jini, rashin cin kayan lambu da 'ya'yan itatuwa yayin da ake cin abinci, kibar da ta wuce kima, cin gishiri fiye da kima yayin cin abinci, shan taba, yawan sukari a cikin jini da dai sauransu.

Masu nazarin sun yi bayanin cewa, babbar illar da gurbatacciyar iksa take haifarwa game da kamuwa da shanyewar jiki, ta wuce zaton mutane sosai, musamman ma illar da take haifarwa a kasashe masu tasowa. A daya hannun kuma, shan taba, cin abincin da bai dace ba, rashin isasshen motsa jiki suna ci gaba da manyan dalilanm da ke haddasa kamuwa da lalurar shanyewar gefen jiki a fadin duniya baki daya. Ma iya cewa, yiwuwar kamuwa da wannan matsala ta shnayewar gefen jiki tana da nasaba da yanayin rayuwa ta hanyar da ta dace, ko kuma ta hanyar da ba ta dace ba. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China