in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sabuwar yarjejeniyar musayan kudi tsakanin Sin da Nijeriya za ta taimakawa 'yan kasuwa
2016-04-24 11:25:29 cri
Zuwa ga sashen Hausa na Rediyon kasar Sin CRI.

Tare da fatan daukacin ma'aikatan ku suna nan lafiya a birnin Beijing kamar yadda nake a lafiya. Hakika, na samu damar sauraron sabon shirin ku na Gani Ya Kori Ji a ranar Laraba 20 ga watan Afrilu, inda malamai Saminu, Maman da Ahmad suka tattauna kan sabbin yarjeniyoyi da aka daddale tsananin kasashen Sin da Nijeriya yayin ziyarar aiki mai cike da tarihi da shugaba Muhammadu Buhari ya kai kasar Sin a makon da ya gabata.

Koda yake, malam sun tattauna kan shawarwari da dama da aka cimma tsakanin kasashen biyu yayin wannan ziyara da suka shafi batun samar da ababen more rayuwa kamar samar da sabbin jiragen kasa, harba sauraron dan Adam da kuma batun bashin tsabar kudi ga Nijeriya har dala biliyan 6. Sai dai ni a nawa bangaren, batun yarjejeniyar nan da aka daddale tsakanin Sin da Nijeriya kan musayar kudin Sin RMB da kuma takardar kudin Nijeriya wato Naira a kasuwannin bankunan kasashen ya fi jan hankali na. Domin akwai dimbin 'yan kasuwar Nijeriya da ke shan faman wahala wajen sauya takardar Naira zuwa dalar Amurka a kasuwar bayan fage kafin su nufi kasar Sin domin sayo haja. Ba shakka, wannan yana kawo tarnaki wajen tafiyar da hada hadar kasuwanci da cinikayya yadda ya kamata, har ila yau matsalar kan haifar da hauhawar farashin kayayyaki musamman a yayin da farashin dalar ya yi tashin gwauron zabi a kasuwar bayan fage.

A zahirin gaskiya, kusan dukkanin kayan haja da ake siyarwa a kasuwannin Nijeriya suna zuwa ne daga kasar Sin, saboda haka matsalar da 'yan kasuwa ke fuskanta wajen musayar kudi ta zo karshe bisa la'akari da wannan sabuwar yarjejeniya mai tagomashin gaske. Wato yanzu 'yan kasuwar Nijeriya za su iya shigar da takardun kudi na Naira a banki kuma su karbi kudin Sin na RMB ba tare da wata matsala ba.

Ina fatan 'yan kasuwar mu za su yi amfani da wannan Kyakkyawar dama wajen kwarara zuwa kasuwannin China domin sayo hajoji masu yawa, lamarin da ba ma kawai zai wadata kasuwannin mu na cikin gida da hajoji ba zai kuma kai ga iya daidaita farashin kayayyaki. Kazalika, ina fatan wannan yarjejeniya za ta taimaka wajen rage gibin cinikayya da ke tsakanin kasar Sin da Nijeriya.

Mai sauraron ku a kullum

Nuraddeen Ibrahim Adam

Shugaban kungiyar

Great Wall CRI Listeners Club

Kanon Dabo, Nigeria

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China