in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shirin kasuwanci, dalibta da soyayya a China ya burge ni matuka
2016-04-18 09:42:58 cri
Zuwa ga sashen Hausa na CRI.

Tare da fatan baki dayan ma'aikatan CRI Hausa suna cikin koshin lafiya a birnin Beijing. Hakika, CRI CIBN ya yi tunani mai kyau wajen shirya wannan shirin bidiyo domin gabatar mana da hakikanin yadda al'ummar Hausawa ke gudanar da kasuwanci, dalibta har ma da soyayya a kasar China. Ba shakka, wannan shirin bidiyo ya kara kusanto da kasar Sin mai tazarar kilomita fiye da dubu 10 ga al'ummar Nijeriya ta hanyar gabatar da shirin bidiyo na farko dangane da rayuwar Hausawa a China. Hakan ya taimaka kwarai da gaske, domin Hausawa suna cewa, Gani Ya Kori Ji.

Shirin dalibta a China da na kalla ya ja hankali na sosai saboda yadda hukumomi a kasar Sin suka yi kyakkyawan tsari ga daliban kasashen wajen domin su iya gudanar da karatunsu cikin 'yanci da walwala. Misali, shirin ba da tallafin kudin karatu ga dalibai da da ke farawa da Yuan 1,300 har zuwa 3,000 kamar yadda dalibi Muhammad Salim Garba ya fada da bakin sa. Wani abu da ya kara burge ni da dalibta a China shi ne kulawa da bukatun dalibai na musamman, kamar yadda na ga jami'oi kasar Sin sun tanadi wajen dafa abinci irin na gida Afirka. Wannan ya sa sauran dalibai kamar su Kabiru Abbati Dankanti da Adamu Muhammad Jajere daga jihar Yobe sun nuna gamsuwar su da yanayin rayuwa a China tamkar yadda takwarorin su mata Maryam Aminu da Zulaihat Muhammad masu koyin aikin likita suka yaba da zaman rayuwar su a China.

Ban da shirin dalibai a China, shi ma shirin kasuwanci a China ya bani sha'awa sosai musamman yadda na kalla, wato al'ummar Hausawa su na yin tururuwa zuwa birnin Guangzhou domin gudanar da harkokin kasuwanci. Misali, dan kasuwa Alhaji Mustapha Hamza wanda ya shafe shekaru da dama a birnin na Guangzhou yana gudanar da harkokin kasuwanci ya alamanta kyakkwan yanayin kasuwanci da kasar Sin ta tanadarwa baki 'yan kasashen waje. Wani matashi dake harkar wayoyin salula a birnin na Guangzhou mai suna Muhammad Bello ya burge ni sosai saboda yadda ya ke mafarkin wata rana ya koma gida Nijeriya ya kafar wata babbar harkar ta wayoyin salula sakamakon kwarewa da ya samu a wannan fanni a birnin Guangzhou.

Idan zan ce wani abu kuwa dangane da shirin soyayya a China, to lallai a ra'ayi na karbuwa da al'ummar Hausawa suka samu daga Sinawa ta kai wani matsayi na koli, domin har an fara samun auratayya a tsakani. Dan asalin jihar Kano Alhaji Sani Tsoho Alasan wanda ya auri Basiniya Halima wani kyakkwan misali ne dangane da wannan lamari. Domin kamar yadda mu ka gani Allah SWT Ya albarkace su da 'ya'ya mata biyu wato Aisha da Hauwa. Kuma wadannan ma'aurata na ci gaba da gudanar da rayuwar su cikin jin dadi da walwala.

A nan ya zama wajibi a yaba wa gidan Rediyon CRI CIBN bisa daukan nauyin shirya da kuma watsa wadannan shiruka masu nishadantarwa game da karin ilimi ta kafofin zamani da suka hada da Facebook da crihausa.com da kuma tashar talbijin ta NTA Startimes kan rayuwar Hausawa a kasar Sin mai nisan gaske. Ba shakka, wannan shiri ya zama abin da ake cewa, gani ya kori ji, domin Hausawa baki sun furta da bakin su kan yadda suke jin dadin gudanar da rayuwar su a China.

Mai sauraron ku a kullum

Nuraddeen Ibrahim Adam

Shugaban kungiyar

Great Wall CRI Listeners Club

Kanon Dabo, Nigeria

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China