in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Cibiyar nazarin ciwon kansa ta kasa da kasa ta gabatar da shawara dangane da yaki da ciwon kansa
2015-01-25 16:22:35 cri


Kwanan baya cibiyar nazarin ciwon kansa ta kasa da kasa da ke karkashin shugabancin hukumar kiwon lafiya ta kasa da kasa wato WHO, ta gabatar da sabuwar ka'idar yaki da ciwon kansa a nahiyar Turai, inda ta baiwa al'ummar kasashen Turai shawara a fannoni 12 game da yaki da ciwon.

Babi na farko da ke cikin wannan ka'ida ya shafi taba, da giya, da yadda ake cin abinci. Inda aka bada shawarar cewa, kada a sha taba, ko yin amfani da ko wane irin kayan taba. Kada a sha taba a gida, tare da goyon bayan hana shan taba a wurin aiki. Ya fi kyau a ci isasshen hatsi, kamar wake, da 'ya'yan itatuwa, da kayayyakin lambu, tare da kauce wa cin abincin da ke samar da yawan karfi fiye da kima, kuma kada a sha lemu mai yawan sukari. Sa'an nan a kauce wa cin kayayyakin nama da yawa, kamar su tsiran alade, da naman alade. Ya fi kyau a daina shan giya. Idan akwai bukata sai a takaita.

Tanade-tanaden da ke cikin babi na biyu kuwa sun hada da ka'idar yaki da ciwon kansa masu nasaba da motsa jiki, da kuma samar da kariya a wurare daban daban. A nan an ba da shawarar cewa, kamata ya yi kowa da kowa ya rika motsa jiki a ko wace rana, tare da kaucewa zama kan kujera cikin dogon lokaci. Sa'an nan ya fi kyau a dauki matakan kimiyya, wajen tabbatar da samun nauyin jiki mai dacewa. Ya zama dole kowa da kowa ya kare kansa daga hasken rana, ta hanyoyi daban daban, musamman ma kananan yara, wadanda ya kamata a ba su kariya daga yawan hasken rana fiye da kima. Har wa yau a wuraren aiki kuma, wajibi ne a yi namijin kokarin kauce wa taba abubuwan da su kan haddasa kamuwa da ciwon kansa, sa'an nan a tabbatar da cewa, yawan abubuwan da suke da nasaba da kamuwa da ciwon kansa, bai wuce yadda aka kayyade a gida ba.

Cibiyar nazarin ciwon kansa ta kasa da kasa, ta kuma bai wa mata shawarar yaki da ciwon kansa, inda ta ce, kamata ya yi iyaye mata su yi iyakacin kokarin shayar da jariransu da nononsu, saboda hakan kan rage barazanar kamuwa da ciwon kansa a nononsu. Ban da haka kuma mai yiwuwa ne yin amfani da sinadarin Hormone, wajen shawo kan cututtuka zai kara barazanar kamuwa da ciwon kansa ga mata.

Bayan haka kuma, cibiyar ta jaddada muhimmancin yin allurar rigakafin ciwon kansa, da kuma yin bincike kan lafiyar mutane domin tabbatar da ba su kamuwa da ciwon kansa. (Tasallah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China