in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
A yankin arewacin jihar Yobe(Yobe North) mun samu ruwan sama tamkar da bakin kwarya
2014-07-07 18:07:42 cri

Bayanda a kasa shafe dogon lokaci cikin yanayin tsananin zafi da karancin ruwan sama a damunar bana a fadin jihar Yobe baki daya, a jiya asabar 05 ga watan Yulin shekara ta 2014, mun samu ruwan sama tamkar da bakin kwarya a jihar Yobe masamman ma a yankin arewacin jihar Yobe inda aka shatata ruwansa tamkar da bakin kwarya, lamarin da ya haddasa malalar ruwan sama a galibin manya da kananan tituna a birane da kauyukan jihar Yobe. Dud da ruwan sama da aka fara samu a karon farko a damunar bana a jihar Yobe, manoma da sauran al'ummar jihar na ci gaba da dukufa wajen gudanar da addu'o'in kara samun ruwan sama a jihar Yobe tare da gudanar da addu'o'in masamman domun samun daurewar ruwan damuna da kuma zaman lafiya a fadin jihar baki daya. Daga karshe, muna fata gwamnatin jihar Yobe da gwamnatin jamhuriyar jama'ar Sin za su rittaba hannu tare da daddale yarjeniyar hadin gwiwa ta fannin harkar bunkasa aikin gona da yaki da gusowar hamada tsakanin Sin da jihar Yobe. Jihar Yobe dai, jiha ce dake fama da gusowar hamada, masamman ma a yankin arewacin jihar Yobe inda gusowar hamadar ke ci gaba da yin illa ga gonaki da gidaje.

Daga Alhaji Ali kiraji Gashua.

Labarai masu Nasaba
Ga wasu
v mun sara muku 2014-07-07 18:06:04
v Sakon gaisuwar fatan alkhairi 2014-07-07 18:03:22
v Yan kabilar Uighur musulmai dake yankin Dinjiang 2014-07-06 18:01:52
v Gasar Cin Kofin Duniya 2014-07-04 08:57:50
v Yaki da masu aikata laifukan cin amanar kasa a kasar Sin 2014-07-03 09:43:51
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China