Wata jaridar Hausa mai suna 'aminiya' dake futowa mako-mako a ranar juma'a, ta buga wani bayani akan kabilar uighur musulmai a kasar Sin. A cikin labarin da ta buga a ranar juma'a 04 ga watan Yuli shekara ta 2014, ta labarta cewa, ma'aikatun gwamnati sun hana musulmi yin azumi a kasar Sin. Labarin da jaridar aminiya ta futar ta kara da cewa, gwamnati a yankin Dinjiang dake yammacin kasar Sin sun hana al'ummar musulmai yan kabilar Uighur yin azumi a wannan wata mai alfarma na Ramadan. Haka nan, jaridar aminiya ta ce, galibin wayanda gwamnati suka hana yin azumi a gurin, malamai da dalibai ne, kana jaridar ta ce, wata kungiyar yan kabilar Uighur sun ce, wasu ma'aikatun suna raba abuncin rana kyau dan hana musulmai a yankin gudanar da aiyukan ibada a wannan wata mai daraja na ramadan. Ko menene gaskiyar wannan labarin?, ina jiran amsa. Domun sau da yawa, wasu kafufin yada labaru na yawaita nuna kiyaiyarsu ga kasar Sin ta bata sunan gwamnatin kasar Sin
Na gode, Naku, Alhaji Ali kiraji Gashua.




