in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Andrea Bocelli zai rera wakar Nessun Dorma a bikin nunin al'adun Asiya
2019-05-15 19:09:45 cri

A yammacin yau Laraba, shahararren mawakin Italiyan nan Andrea Bocelli zai rera wakar wasan kwaikwayon Turandot mai suna Nessun Dorma yayin bikin nunin al'adun Asiya.

Jiya da yamma ne Andrea Bocelli ya bayyana a wurin atisayen bikin dake gudana a filin wasannin na Bird's Nest yayin da yake zantawa da wakilin babban rukunin gidajen rediyo da telibijin na kasar Sin wato CMG a takaice cewa, wakar Nessun Dorma tana da muhimmanci a bangaren wasan kwaikwayon duniya. Ya sha rera wakar a kasar Sin, yanzu haka zai sake rera wakar a filin nunin al'adun Asiya mai muhimmanci matuka.

Andrea Bocelli ya kara da cewa, kide-kiden kasar Sin suna taka babbar rawa a dandalin kide-kiden duniya, sanin kowa ne cewa, Sinawa suna kishin kide-kiden kwarai.

Ya ce, yayin ziyararsa a kasar Sin, ya kara fahimtar muhimmancin cudanyar wayewar kai tsakanin kasa da kasa, saboda kide-kide harshe ne da al'ummun kasashen duniya suke yin cudanya maras shinge, a don haka kide-kide za su taimaka wajen fahimtar juna tsakanin al'adu dabam dabam, kuma wani bangare ne na tushen tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a fadin duniya.(Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China