in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Majalisar sojojin Sudan ta ce wasu mutane da suka kai hari kan masu zanga zanga sun kashe soja guda
2019-05-14 10:05:51 cri
Majalisar mulkin rikon kwarya ta sojojin Sudan (TMC) ta sanar cewa, wasu kungiyoyin da ba'a san ko su wanene ba sun kaddamar da hari kan masu zanga zanga dake zaman dirshan a Khartoum inda suka hallaka wani jami'in soja guda da kuma jikkata wasu sojojin uku da fararen hula masu yawa.

"Akwai wasu bangarori dake neman hargitsa juyin juya halin kasar sakamakon irin nasarorin da aka cimma kawo yanzu, suna ci gaba da yunkuri wargaza yarjejeniyar da aka riga aka cimma domin jefa kasar cikin rudani," TMC ta bayyana hakan cikin wata sanarwa.

Wasu kungiyoyin da ba'a tantance su ba sun yi ta harba bindiga kan mai tsautsayi inda suka hargitsa yanayin tsaro a ciki da wajen inda masu zanga-zangar suke zaman dirshan," suna cin mutuncin fararen hula da dakarun sojojin dake bada kariya ga masu zanga-zangar," in ji sanarwar.

Majalisar sojojin ta sha alwashin yin aiki tare da bangarorin 'yan adawa na Freedom da Change Alliance domin daukar matakan shawo kan halin da ake fuskanta. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China