Cikin wata sanarwa, mai gabatar da karar ya gabatarwa kotu batun kisan Babikir wanda jami'an tsaro suka hallaka a yankin Buri. Ya kuma bukaci kotun da ta gaggauta bincikar dukkanin kararrakin kisan masu zanga zangar kasar ta baya bayan nan.
Kafin hakan, mukaddashin babban mai shari'ar kasar Al-Waleed Sid-Ahmed Mahmoud, ya ba da umarnin yiwa al-Bashir tambayoyi, game da zargin safarar kudaden haram, da tallafawa 'yan ta'adda da kudade.
Tuni dai shugaban majalissar soji mai rikon kwarya a Sudan Abdel-Fattah Al-Burhan, ya ce aikin majalissar shi ne jan ragamar kasar na wani lokaci, bayan hambarar da tsohuwar gwamnatin al-Bashir. (Saminu Alhassan)