Firaministan Sin ya yi kira da a kara kwazo wajen daga martabar tambarin kasar Sin
Firaministan kasar Sin Li Keqiang, ya yi kira da a kara kwazo wajen daga martabar tambarin hajojin kasar Sin a dukkanin kasashen duniya, ta hanyar bunkasa kwarewa da sanin makamar aiki. Li Keqiang ya bayyana hakan ne cikin wani sakon umarni da ya aike a Juma'ar nan, ga taron ranar tambarin kasar Sin wanda aka bude a birnin Shanghai.
Ya ce karfafa kimar tambarin Sin, da bunkasa sashen masana'antun sarrafa hajoji, da inganta sashen ba da hidima na da muhimmancin gaske, wajen bunkasa harkokin sayayya a cikin gida, da bunkasa ci gaba mai ma'ana.
Taron ranar tambarin kasar Sin wanda aka bude a birnin Shanghai, zai gudana tsakanin ranekun 10 zuwa 12 ga watan nan na Mayu.