Wang Yi ya bayyana hakan ne, yayin da ya halarci taron bude dandalin kasa da kasa na shekarar 2019 na hadin gwiwar kasashen uku a Juma'ar nan.
Ya ce bana ake cika shekaru 20 da kulla huldar kawancen sassan uku, wato Sin da Japan da Koriya ta Kudu, don haka a cewar sa, kawancen sassan uku ya kai wani sabon matsayi a tarihi. Ya kara da cewa, Sin a shirye take ta yi aiki tare da Japan, da Koriya ta Kudu wajen bunkasa hade shiyyar su da ci gaban ta baki daya.