in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin ta fitar da sanarwa game da shirin Amurka na kara sanya haraji kan kayayyakinta
2019-05-09 08:55:18 cri

Kasar Sin ta bayyana takaicinta kan matakan Amurka na kara yawan harajin da za ta sanya kan kayayyakin kasar Sin dake shiga cikin Amurka, tana mai cewa, karuwar takaddamar cinikayya tsakanin sassan biyu, ya saba muradun al'ummomin kasashen da ma duniya baki daya.

A jiya ne dai, kasar Sin ta bayyana hakan cikin wata sanarwa da ta rabawa manema labarai, bayan da Amurka ta sanar da cewa, daga ranar 10 ga watan Mayu, za ta kara yawan haraji daga kaso 10 zuwa 25 cikin 100 kan kayayyakin kasar Sin da darajarsu ta kai dala biliyan 200.

Sai dai kasar Sin ta bayyana rashin jin dadinta matuka, tana mai cewa, idan har matakin sanya harajin Amurka ya fara aiki nan take, hakan ka iya tilastawa kasar Sin mayar da martanin da ya dace.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China