in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin ta nuna rashin amincewa ga takunkumin da Amurka ta sanya kan Iran
2019-04-23 19:26:30 cri

Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Geng Shuang, ya ce kasashen duniya ciki har da kasar Sin, suna gudanar da hadin gwiwa cikin adalci dake tsakaninsu da kasar Iran a bangaren makamashi bisa tsare-tsaren dokokin duniya, kuma dole ne a martaba, tare kuma da kiyaye hakan, a don haka kasar Sin ta nuna rashin amincewa ga takunkumin da Amurka ta sanyawa kasar Iran a gefe guda, haka kuma ba ta amince da dokar da Amurka take amfani da ita domin hukunta wasu batutuwan dake shafar Iran a cikin kasarta ba.

Geng Shuang ya bayyana hakan ne, yayin taron ganawa da manema labaran da aka saba yi a nan birnin Beijing yau Litinin.

A kwanan baya sakataren harkokin wajen Amurka Mike Pompeo ya sanar da cewa, tun daga ranar 2 ga watan Mayun bana, Amurka ba za ta ba da kariya ga wadanda za su sayi mai daga Iran ba, kuma ta bukace su da su daina shigo da mai daga Iran, in ba haka ba, za su fuskanci takunkumin daga gare ta.

Geng Shuang ya kara da cewa, matakin da Amurka ta dauka zai kara tsananin tangarda a yankin Gabas ta Tsakiya, da kuma kasuwar makamashin duniya, don haka kasar Sin ta bukaci Amurka da ta dauki matakin da ya dace, kada ta dauki matakin da zai lalata yanayin da ake ciki.(Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China