in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin na fatan Amurka za ta kauracewa yamutsa hazo game da alakar Sin da Latin Amurka
2019-04-16 10:29:20 cri

Kasar Sin ta ce bai dace ba Amurka ta yi kokarin yamutsa hazo, game da alakar Sin din da kasashen Latin Amurka. Wannan tsokaci na zuwa ne daga mahukuntan Sin, bayan da sakataren wajen Amurka Mike Pompeo ya yi wani shagube game da hakan, yayin wata ziyara da ya kai kasar Chile.

Da yake tsokaci game da hakan, kakakin ma'aikatar wajen Sin Lu Kang, ya ce abu ne da bai dace ba ga Amurka, ta yi kokarin kunna wata wuta game da alakar Sin da kasashen Latin Amurka, kuma ko alama Sin ba za ta lamunci hakan ba.

Lu Kang ya ce, alakar Sin da kasashen Latin Amurka, an gina ta ne bisa ka'idojin martaba juna, da daidaito, da cimma moriya tare, da ciyar da juna gaba, da samar da tallafi domin ingiza tattalin arziki, da kyautata zamantakewar juna tsakanin al'ummun sassan biyu.

Ya ce, tsawon lokaci, kasar Amurka na daukar kasashen dake Latin Amurka a matsayin wasu unguwannin bayan garin ta, inda take matsa musu lamba, da tsoratar da su, ta kuma hambarar da gwamnatocin wasu ma daga cikin su. To sai dai a nata bangaren, a cewar jami'in, Sin na da imanin cewa, kasashen Latin Amurka za su dauki matakin da ya dace, na nunawa duniya wane ne aboki na gari da wanda ya sabawa hakan, da sashen dake bin ka'idojin doka da oda, da mai kokarin karya su.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China