in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ana sa ran Sin da Amurka za su kara taka rawa a cikin harkokin duniya
2019-04-06 16:12:57 cri

Shugaban Amurka Donald Trump, ya gana da Liu He, mamban hukumar siyasa ta kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin, kana mataimakin firayin ministan kasar kuma jagoran bangaren kasar Sin a tattaunawar tattalin arziki dake tsakaninta da Amurka, wanda ke halartar tattaunawar manyan jami'an kasashen biyu karo na 9 a birnin Washington. Yayin ganawar da aka yi ranar Alhamis da ta gabata, Donald Trump ya ce, yana fatan tawagogin sassan biyu za su daddale yarjejeniya da wuri, saboda zai amfanawa kasashen biyu, da ma daukacin kasashen duniya. Kana yayin da yake amsa tambayar da mai yin sharhi kan harkokin duniya na babban rukunin gidajen rediyo da talebijin na kasar Sin CMG ya yi masa game da sauke nauyi a cikin harkokin duniya, shugaba Trump ya bayyana cewa, wannan batu ne mai muhimmanci ga kasashen Sin da Amurka.(Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China