A cewar ma'aikatar, a lokacin hutun da aka fara ranar Laraba zuwa jiya Asabar, bangaren yawon bude ido, ya samu ribar da ta kai Yuan biliyan 117.67, kwatankwacin dalar Amurka biliyan 17.48, karuwar kaso 16.1 cikin 100.
Alkaluma na nuna cewa, iyalai sun fi ziyartar wuraren yawon bude ido, lamarin da ya bunkasa sashen al'adu, shakatawa da hidimar abinci da wuraren kwana.(Ibrahim)