Yayin taron majalisar gudanarwar kasar da firaministan kasar Li Keqiang ya jagoranta a jiya Talata, an yanke shawarar cewa, za a samar da wani asusu na musamman domin aiwatar da shirin horas da sana'o'in hannun.
Taron ya kuma bayyana cewa, za a sanar da jama'a kan yadda aka yi amfani da kudade da ma sauran muhimman bayanai kan wannan shiri, a hannu guda kuma za a hukunta wadanda suka yi karyar shiga wannan horo domin su samu kudi kamar yadda doka ta tanada.
Bugu da kari, za a taimakawa manufofin kananan hukumomi game da tallafin samun horon, kana ma'aikatan da suka cancanta za su iya shiga shirye-shiryen samun horo su kuma karbi tallafi.
Taron ya kuma jaddada cewa, wajibi ne a mayar da hankali ga ingancin horon, da kara daga matsayin shiryen-shiryen koyar da sana'o'in. (Ibrahim)