in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Firaministan kasar Sin ya halarci taron shugabannin kasashen Sin da yankunan tsakiya da gabashin Turai karo na 8
2019-04-13 16:59:39 cri

Firaministan kasar Sin Li Keqiang, ya halarci taron shugabannin kasashen Sin da yankunan tsakiya da gabashin Turai karo na 8 a birnin Dubrovnik na kasar Croatia, inda shugabannin kasashe 16 na tsakiya da gabashin Turai suka halarta. Yayin taron na jiya Juma'a, an kuma yi maraba da kasar Girka da ta shiga hadin gwiwar da ke tsakanin kasar Sin da kasashe 16 na yankunan 2 na Turai, inda Tarayyar Turai wato EU da kasashen Austria da Belarus da Switzerland da Bankin Rayawa Da Farfado Da Nahiyar Turai wato EBRD suka aike da 'yan kallo.

A cikin jawabinsa, Li Keqiang ya yaba wa nasarorin da aka samu karkashin hadin gwiwar kasar Sin da kasashe 16 na tsakiya da gabashin Turai. Ya kara da cewa, a kwanakin baya, an yi taron shugabannin kasashen Sin da kungiyar EU karo na 21 cikin nasara, inda bangarorin 2 suka ba da sanarwar hadin gwiwa mai kunshe da batutuwa da dama. Ya ce hadin gwiwa tsakanin kasar Sin da kasashe 16 na tsakiya da gabashin Turai, wani bangare ne na huldar da ke tsakanin Sin da Turai, wadda take kara azama ga dinkewar Turai baki daya da bunkasar huldar da ke tsakanin bangarorin 2.

Firaministan Sin ya kuma sanar da cewa, za a shirya taron karo na 9 a kasar Sin a shekara mai zuwa. Kuma yana sa ran shugabannin kasashen za su halarta, inda za su iya tsara shirin raya hadin gwiwar dake tsakaninsu a mataki na gaba. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China