A jiya Talata ne, firaministan kasar Sin Li Keqiang ya isa kasar Croatia, don fara wata ziyarar aiki a kasar tare da halartar taron shugabannin Sin da kasashen gabashi da tsakiyar Turai (CEEC) karo na 8, taron da zai gudana a birnin Dubrovnik na kasar ta Croatia dake bakin ruwa.
Li shi ne firaministan kasar Sin na farko da ya ziyarci kasar Croatia, tun lokacin da kasashen biyu suka kulla huldar diflomasiya a tsakaninsu shekaru 27 da suka gabata.
Kafin ya isa Zagbreb, zango na biyu na ziyarar aikin da yake yi a nahiyar Turai, Mr. Li ya kuma kammala ziyarar da yake a Brussels tare da halartar taron shugabannin Sin da EU karo 21 cikin nasara. (Ibrahim)