in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An gwabza fada a filin hakar mai mafi girma na Libya
2019-04-30 09:27:58 cri

Kamfanin mai mallakar kasar Libya NOC, ya bayyana takaicin sa game da barkewar musayar wuta tsakanin sassan da ba sa ga maciji da juna a kasar, a yankin Sharara mai kunshe da filin hakar danyen mai mafi girma dake kasar.

Wata sanarwa da kamfanin na NOC ya fitar a jiya Litinin, ta ce mayaka sun gwabza fada a yankin rijiyar mai mai lamba 186, inda aka rika jin karar harbin rokar harba gurneti.

Ko da yake dai sanarwar ta ce ba a samu asarar rayuka sakamakon aukuwar lamarin ba, amma a hannu guda, NOC na fatan dukkanin sassan da batun ya shafa za su kai zuciya nesa, su kuma dakatar da bude wuta a daukanin filayen samar da makamashi dake kasar.

Sharara dai na da nisan kilomita 900 kudu da birnin Tripoli, fadar mulkin kasar. Ana kuma hakar danyen mai da yawan sa ya kai ganga 300,000 a ko wace rana daga filin.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China