in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Bakin haure 130 aka tusa keyarsa daga Libya zuwa Nijer
2019-01-30 09:29:57 cri

Hukumar kula da 'yan gudun hijira ta MDD (UNHCR) ta bayyana cewa, kimanin bakin haure 130 ne aka tusa keyarsu daga kasar Libya zuwa Jamhuriyar Nijer.

A wata sanarwar da hukumar ta UNHCR ta fitar ta ce, 'yan gudun hijirar 130 sun fito ne daga kasashen Sudan, Habasha, Eritrea, da Somalia wadanda aka tsugunar da su a cibiyar dake Tripoli, inda daga bisani aka kwashe su zuwa cibiyar hukumar UNHCR dake Niamey ta kasar Nijer.

Libya ta kasance a matsayin wata cibiyar da bakin haure ke amfani da ita ta tekun Mediterranean, inda suke tsallakawa zuwa kasashen Turai sakamakon matsalar tabarbarewar tsaro da tashe tashen hankula a kasar ta arewacin Afrika tun bayan da kasar ta fada rikici a shekarar 2011 wanda ya yi sanadiyyar kifar da gwamnatin tsohon shugaban kasar Muammar Gaddafi.

Wuraren zama a Libya sun cika makil da dubban bakin haure ta barauniyar hanya wadanda dakarun tsaron tekun Libyan suka ceto su a gabar tekun kasar.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China