in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Majalisar wakilan Libya ta bukaci a haramta ayyukan kungiyar Muslim Brotherhood
2019-01-28 10:05:40 cri

Baki dayan mambobin majalisar wakilan kasar Libya su 20 dake gabashin kasar, a ranar Lahadi sun bukaci a gudanar da zaman majalisar wanda zai kada kuri'ar haramta ayyukan kungiyar Muslim Brotherhood a Libyan.

"Mu, tare da sauran al'ummar kasar Libya, mun goyi bayan abin da shugaban majalisar kasa Khalid al-Meshri ya bayyana a matsayin yin murabus daga kungiyar Muslim Brotherhood a Libya, inda ya yi ikirarin cewa, kungiyar ta gaza kawo sauye sauyen da ake bukata," in ji sanarwar.

"Mambobin majalisar wakilan da wadanda suka sanya hannu kan wannan sanarwar sun bukaci kakakin majalisar wakilan da kada kuri'ar haramta ayyukan kungiyar 'yan uwa musulmi ta Muslim Brotherhood da bayyana kungiyar a matsayin kungiyar 'yan ta'adda." in ji sanarwar.

Mambobin majalisar su 20 sun bayyana cewa, kungiyar tana goyon bayan ayyukan ta'addanci tun da farko, ko a yankunan Benghazi, Darna ko kuma wani waje na daban, wanda ya shafi ba su tallafin kudi, da harkar siyasa, da kuma kafofin yada labarai.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China