in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Guterres ya yi kira da a kara taimakawa wadanda guguwar Kenneth ta aukawa
2019-04-29 09:47:24 cri

Babban magatakardar MDD Antonio Guterres, ya ce ya yi matukar kaduwa, da jin asarar rayuka da dukiyoyi da aka samu a kasashen Mozambique da tsibirin Comoros, sakamakon mahaukaciyar guguwar nan ta Kenneth da ta aukawa kasashen.

Cikin wata sanarwa, kakakin babban magatakardar MDDr Stephane Dujarric, ya rawaito Guterres na bayyana damuwa game da aukuwar wannan ibtila'i. Sanarwar ta ce, makwanni 6 ke nan da aukuwar bala'in guguwar Idai a Mozambique, da Malawi da Zimbabwe, sai ga shi kuma an sake fuskantar wani yanayi mai tayar da hankali.

Sanarwar ya kuma ce, Mr. Guterres, na mika sakon ta'aziyya da goyon baya ga iyalai da gwamnatocin al'ummun da wannan ibtila'i ya shafa a Mozambique da Comoros.

Daga nan sai ya gabatar da kokon bara ga al'ummun kasa da kasa, game da bukatar samar da karin gudummawa da ake tsananin bukata a halin yanzu, da ma wadda za a bukata a nan gaba.

Har yanzu dai kasar Mozambique na kokarin murmurewa daga ta'adin da guguwar Idai ta haifar a tsakiyar watan Maris da ya gabata, yayin da kuma guguwar Kenneth ke haifar da sabuwar barazana ga kasar.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China