in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Guguwa da ambaliyar ruwa ta Idai ta hallaka sama da mutane 200 a kudu maso gabashin Afirka
2019-03-20 09:53:21 cri

Ofishin MDD mai lura da ayyukan jin kai ko OCHA, ya ce sama da mutane 200 sun rasa rayukan su, kuma adadin na iya karuwa, bayan da guguwa mai karfi da ambaliyar ruwa da aka yiwa lakabi da "Idai" ya ratsa sassan kudu maso gabashin nahiyar Afirka.

Da yake tsokaci game da aukuwar wannan annoba, mataimakin kakakin babban magatakardar MDD Farhan Haq, ya ce a kasar Mozambique, a kalla mutane 84 ne aka tabbatar da rasuwar su sakamakon ibtila'in, kuma akwai yiwuwar adadin ya karu a nan gaba.

Farhan Haq, ya yi wannan karin haske ne yayin taron manema labarai da aka saba gudanarwa. Yana mai cewa, Beira, birnin dake da mutane kusan 500,000, shi ne wuri da bala'in ya fi yiwa barna.

A kudancin kasar Malawi ma, guguwa da ambaliyar ruwan sun tafka barna mai yawa. Har ila yau ambaliyar ruwa na ci gaba da tafka barna a yankunan kasar Zimbabwe.

Ofishin OCHA ya ce, bisa alkaluma daga gwamnatin Malawi, bala'in "Idai" ya shafi mutane kimanin 922,900, ciki hadda mutane 56 da aka tabbatar da rasuwar su, da wasu mutanen 577 da suka jikkata. Bugu da kari, akwai wasu karin mutanen sama da 82,700 da suka rasa matsugunnan su, yayin da mutane da dama suka fada yanayi na bukatar tallafin jin kai a yankuna da bila'in ya fi tsanani.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China