in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Guguwar Idai na daga cikin annoba mafi muni da suka aukawa kudancin Afrika
2019-03-21 10:13:29 cri

MDD ta ce, mahaukaciyar guguwar Idai da ta yi sanadin mutuwar mutane a kalla 360, ka iya zama daya daga cikin munanan annobar da suka aukawa yankin kudancin Afrika a tarihi.

Mataimakin kakakin majalisar Farhan Haq ya gabatar da rahoto mai tayar da hankali game da irin asarar da guguwar ta haifar a sassan kasashen Malawi da Mozambique da Zimbabwe.

Farhan Haq ya bayyana wa taron manema labarai da aka saba yi cewa, kawo yanzu ba a san abun da ake bukata ba, saboda yawan asarar da guguwar ta haifar, sannan kuma an kasa isa yankunan.

Ya ce, jami'an dake kula da ayyukan jin kai na majalisar, sun sanar da cewa, shugaban hukumarsu Mark Lowcock, ya ware dala miliyan 20 daga asusun ba da agajin gaggawa na majalisar, domin dorawa kan kokarin gwamnatocin Mozambique da Zimbabwe da Malawi, na taimakawa al'ummomin da annobar ta shafa.

Kusan mutane miliyan 1 ne al'amarin ya shafa a Malawi, inda mutane 56 suka mutu, wasu 577 kuma suka raunana. Sannan sama da mutane 82700 ne suka rasa matsugunansu.

A cewar gwamnatin Mozambique kuwa, a kalla mutane 202 ne aka tabbatar sun mutu, inda kakakin na MDD ya ce, akwai yiwuwar samun karuwar adadin. Baya ga haka, asusun kula da kananan yara na MDD UNICEF, ya ce yara 260,000 ne annobar ta shafa a kasar.

A kalla mutane 102 ne suka mutu, yayin da wasu 200 suka raunana a kasar Zimbabwe, inda kuma rahotanni suka ce har yanzu ba a ga kimanin mutane 200 da suka bata ba.

Farhan Haq ya ce, manyan motoci dauke da kayayyakin shimfida da ruwa da kayayyakin da ba na abinci ba da kayayyakin tsafta sun isa yankunan da lamarin ya shafa a Zimbabwe, kuma tuni aka fara rabo a wasu wuraren. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China