Babban sakataren MDD Antonio Guterres ya bayyana cewa, mahaukaciyar guguwar Idai, da ta aukawa kasashen Mozambique da Zimbabwe da Malawi, ta halaka mutane a kalla 700.
Guterres wanda ya bayyana hakan a jiya Talata, ya kuma yi kira ga kasashen duniya, da su agazawa kasashen da iftila'in ya shafa da gudummawar dala miliyan 281.7.
Jami'in na MDD ya ce, yawan wadanda suka mutu a kasashen uku, ya kai a kalla 700, baya wasu daruruwa da suka bace. An kuma yi kiyasin mutane miliyan 3 da bala'in ya shafa, kusan kaso biyu bisa uku na wannan adadi ya shafi kasar Mozambique ne.
Mahaukaciyar guguwar Idai mai tafe da iska da ruwan sama, na daya daga cikin bala'u da nahiyar ta fuskanta a tarihi. (Ibrahim)